Abubuwa hudu da za a iya tuna Khalifa Isyaka Rabi'u da su

Janaizar Khalifa Isyaka Rabiu
Bayanan hoto, Dubban mutane ne suka halarci jana'izar marigayin a birnin Kano

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u, wanda ya rasu a ranar Talata a birnin London, sannan aka yi jana'izarsa a birnin Kano ranar Juma'a, mutum ne da ya shahara kan abubuwa da dama.

Allaha ya yi masa tsawon rai inda ya rayu shekara 93, kuma duk da cewa ya yi fama da rashin lafiya musamman ciwon kafa, za a iya cewa ya ci gaba da gudanar da al'amuransa na rayuwa har lokacin da ya koma ga Allah.

Ya rasu ya bar mata hudu da 'ya'ya 63 da kuma jikoki da dama cikinsu har da Alhaji Abdussamad Isyaka Rab'iu, wanda shi ne shugaban hadakar kamfanin BUA.

Mun yi nazari kan wasu daga cikin abubuwan da za a iya tuna marigayin da su:

1. Karatun AlKur'ani

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya yi karatun AlKur'ani da na adidni a birnin Kano, kafin daga bisani aka tura shi birnin Maiduguri na jihar Borno domin kara karatu.

Hafizi ne kuma malami ne domin ya karantar da dalibansa, sannan ya yi suna wajen hada kan almajiransa a karatun AlKur'ani a kodayaushe, bayan sauka da ake yi kusan a kullum a gidansa.

Ya yi kokari sosai wajen bunkasa karatun AlKur'ani, hakan ya sa har aka yi masa lakabi da Malam mai Tabaraka.

Shi ne malamain da ya gina babban masallacin da har ake sallar Juma'a a cikin gidansa.

Ficensa a ilimin Alku'ani da yi masa hidima ne ya sa ake masa lakabi da "Khadimul Kur'an".

2. Kasuwanci da Malanta

Shi ne malamin da ya hada kasuwanci da malanta, ba kamar sauran malamai ba da suke rike malanta kawai.

A farko 1950 Mallam Isyaka Rabi'u ya fara kasuwanci, duk da cewa bai bar koyarwa ba.

Ya kafa wani kamfani mai suna Isyaku Rabiu & Sons a 1952.

Khalifa Isyaka Rabi'u tare da abokinsa shararrarren dan kasuwa Marigayi Nababa Badamasi

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Khalifa Isyaka Rabi'u tare da abokinsa shararrarren dan kasuwa Marigayi Nababa Badamasi

Da farko kamfanin ya fara da zama dilan kayan kamfanin UAC ne, wanda a wancan lokacin yake kasuwancin kekunan dinki, da litattafan addinin Musulunci da kuma kekuna.

A 1958, kamfanin ya sami bunkasa bayan da aka kafa masakar Kaduna Textile Limited kuma kamfanin na Isyaku Rabiu & Sons ya zama daya daga cikin dilolinsa na farko.

Marigayin ya zama babban dilan kamfanin na UAC a arewacin Najeriya, kuma a 1963 shi da wasu 'yan kasuwa daga Kano suka hadu don kafa Kano Merchants Trading Company.

Wannan kamfanin ya jure wa gasa daga kamfanonin da ke shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Ya kuma kafa wani kamfani mai dinka kayan sawa a 1970.

3. Taimakon al'umma

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama, ciki har da taimakon al'umma.

Khalifan ya yi amfani da kudinsa wajen yi wa addini hidima ta hanyar gina masallatai da makarantu a birnin Kano da kewaye.

Marigayin ya kuma yi suna wurin tallafawa marayu da marasa galihu, inda har gina gidaje ya ke ga almajiransa da ma marasa karfi.

Marigayin, wanda amini ne ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, da Alhaji Aminu Dantata, yana daga cikin fitattun dattawan da suka rage a jihar.

4. Hada kan Musulmi

Khalifa Isyaka Rabu'u da shugaban kungiyar 'yan Izala na Najeriya, Sheikh Bala Lau, a wata ganawa da suka yi

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Khalifa Isyaka Rabu'u da shugaban kungiyar 'yan Izala na Najeriya, Sheikh Bala Lau, a wata ganawa da suka yi

An ba shi mukamin Khalifan darikar Tijjaniya a Najeriya a shekarar 1994, saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.

Hakan ya ba shi damar fada aji da kuma kokarin hada kan musulmai daga dariku daban-daban.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa mutanen da suke bin dariku daban-daban kamar Izala da Kadriyya da Tijjiniya sun hada kansu sun zauna da juna lafiya.

Yana kuma nusar da su cewa duk addini daya ake bi na Musulunci.

Karin labaran da za ku so ku karanta game da Marigayin

Grey line

Tarihin Kahlifa Isyaka Rabi'u

  • Bayanai sun nuna cewa an haifi marigayin ne a 1925
  • Ya yi karatun AlKur'ani da na adidni a birnin Kano
  • Kafin daga bisani a tura shi birnin Maiduguri na jihar Borno domin kara karatu
  • Ya koma Kano inda ya ci gaba da koyar da karatun Kur'ani da na addini
  • Daga baya ne kuma ya fara harkokin kasuwanci inda ya kafa kamfanin Isyaka Rabiu & Sons
  • Ya yi fifce matuka a fagen kasuwanci da na karatun Alkur'ani
  • Daga bisa ni an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya
  • Harkokin kasuwancin da 'ya'yansa suka gada kuma suka ci gaba da samun daukaka a kai
Grey line

Bayani kan darikar Tijjaniya

Mabiya darikar Tijjaniya

Asalin hoton, Getty Images

  • An kafa darikar ne a kasar Aljeriya a shekarar 1784
  • Sheikh Ahmad ibn Muhammad al-Tijjani ne ya kafa ta
  • Ta yadu zuwa sassan duniya daban-daban, inda ta ke da mafi yawan mabiyanta a Arewaci da kuma Yammacin Afirka
  • Tana kuma da karin mabiya a Afirka Ta Kudu, da Indunisiya da kuma sauran sassan duniya
  • Akwai sauran dariku na Sufaye a addininin Musulunci amma Tijjaniya ta fi kowacce girma
  • Sun ce suna da muhimman ayyukan ibada guda uku a kowace rana:
  • Neman gafarar Allah; Yin salati ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kadaita Allah
  • Sai dai ana zarginsu da wuce gona da iri wurin nuna soyayya ga Shehunnansu, lamarin da wasun su ke musanta wa
  • Ana alakanta Sheikh Ibrahim Nyass da farfado da darikar a karni na 20 bayan ta kwanta dama
  • An haife shi a kasar Senegal kuma jama'a kan yi tattaki daga sassan nahiyar da dama domin ziyartar kabarinsa
  • Darikar Tijjaniya ta kasu kashi-kashi musamman a kasashe irin su Najeriya inda suke da mabiya sosai